Isa ga babban shafi
Spain

Mourinho ya karyata labarin ficewa Real Madrid

Kocin Real Madrid Jose Mourinho ya karyata labarin da Jaridar Marca ta buga cewa zai yi ban kwana da Real Madrid a karshen kakar wasa. A jiya Litinin ne jaridar ta ruwaito cewa shugaban Real Madrid Florentino Perez da Mourinho sun cim ma matsaya akan ficewar shi a karshen kakar wasa.

José Mourinho. kocin Real Madrid a spain
José Mourinho. kocin Real Madrid a spain REUTERS/Yorgos Karahalis
Talla

Wasu Rahotanni masu karo da juna suna alakanta ficewar Mourinho a Real Madrid don ya gaji Sir Alex Ferguson a Manchester United.

Yayin da a daya bangaren kuma wasu rahotanni ke cewa Mourinho zai fice ne saboda halin da Real Madrid ke ciki a La liga a bana domin tazarar maki 11 ne tsakaninsu da Barcelona.

Amma kuma Mourinho ya karyata haka yana mai cewa babu wani sabani tsakanin shi da shugaban Real Madrid.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.