Isa ga babban shafi
Champions League

Chelsea za ta nemi tsira, Messi zai nemi kafa tarihi

Kungiyar Cheslea da ke rike da kofin gasar zakarun Turai Za ta nemi tsira daga ficewa daga gasar tun a zagayen farko kuma za ta kasance kungiya ta farko da zata fice mai rike kofin gasar tun a zagayen Farko.

Dan wasan Barcelona Lionel Messi ya zira kwallo a raga a bugun daga kai sai mai tsaron gida
Dan wasan Barcelona Lionel Messi ya zira kwallo a raga a bugun daga kai sai mai tsaron gida REUTERS/Gustau Nacarino
Talla

A makwanni biyu da suka gabata Chelsea ta sha kashi ne hannun Juventus, al’amarin da yasa kungiyar ta sallami kocinta Roberto Di Matteo.

Sai dai har yanzu kwalliya bata biya kudin Sabulu ba bayan daukar Benitez domin ya buga wasanni uku ba tare da nasara ba a Premier.

A yau Laraba idan har Shakhtar Donetsk da Juventus suka yi kunnen doki ko aka tashi wasan babu ci Chelsea ta fice gasar koda ko kwallaye 100 ta zira a ragar FC Nordsjaelland.

Chelsea dai za ta yi fatar Shakhtar ta doke Juventus tare da fatar samun galabar FC Nordsjaelland.

A yau ne kuma Messi na Barcelona zai iya yin kafada da Mueller idan har ya zira kwallo daya a raga, idan kuma dan wasan ya zira kwallaye Biyu zai kafa tarihi ne a matsayin wanda ya fi kowa zira kwallaye a raga a kakar wasa.

A shekarar 1972 ne dai Mueller ya zira kwallaye 85 a raga, kuma a bana Messi ya zira kwallaye 84, tazarar kwallo daya tsakaninshi da Mueller.

A yau dai Barcelona za ta kara ne da Benfica wacce ke neman tsallakewa.

Bayern Munich da Valencia dukkaninsu sun tsallake kuma a yau za su nemi jagorancin Rukuninsu ne inda Bayern za ta kara da Bate, Valencia kuma ta sake kece raini da Lille.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.