Isa ga babban shafi
Wasan Tennis

Djokovic da Serena Williams sun zama gwarazan shekarar 2012 a wasan Tennis

Hukumar wasan kwallon Lambu ko kuma Tennis ta duniya, ta bayyana dan wasan kasar Serbia, Novak Djokovic da ‘Yar wasan kasar Amurka, Serena Williams, a matsayin gwarazan duniya, domin irin bajintar da suka nuna a fagen wasan Tennis a shekarar 2012.

Novak Djokovic (Hagu) da Serena Williams (Dama)
Novak Djokovic (Hagu) da Serena Williams (Dama)
Talla

Dan shekaru 25, Djokovic shi ne ya kasance a saman teburin kwararrun ‘yan wasan Tennis na duniya bayan ya lashe gasar Australian Open kana kuma ya buga wasannin karshe na French Open da US Open.

Wannan dai shi ne karo na biyu da ake bashi wannan matsayi na gwarzon wasan Tennis din duniya a jere a bangaren maza.

Ita kuwa Serena Williams, ‘Yar shekaru 31 a wannan shekarar yawan kyautukan da ta samu daga gasar Grand Slams ya kai 15 bayan ta lashe gasar Wimbledon da US Open.

Har ila yau a bangaren mata it ace ta kasance a saman teburin kwararru a fagen Tennis, baya ga kyautar zinare guda biyu da ta samu a gasar Olympics da aka yi a London.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.