Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Chelsea ta lallasa Leeds United ci 5 da 1

Rafael Benitez ya samu shedawa a jiya Laraba bayan Chelsea ta lallasa Leeds United ci 5-1 wanda kuma yaba ‘Yan wasan shi damar buga wasan kusa da karshe a gasar Carling da Swansea City.

'Yan Wasan Chelsea suna murnanr zira kwallo a raga
'Yan Wasan Chelsea suna murnanr zira kwallo a raga Reuters
Talla

A bana dai Chelsea ta yi hasarar kofuna da dama kama daga kofin Super cup na Turai da Community Shield da kofin Duniya na kungiyoyin kwallon kafa, sannan yanzu haka ta fice gasar zakarun Turai kamar yadda akwai tazara mai nisa tsakaninta da Manchester United da ke jagoracin Teburin Premier.

Don haka wanna kofin na Carling shi ne a gaban Chelsea a yanzu.

A Italia kuma Lazio da Florentina sun tsallake zuwa zagayen Quarter Final a gasar cin kofin kasar amma Napoli ta sha kashi ne hannun Bologna ci 2-1.

A gasar cin kofin kasar Jamus kuma mai rike da kofin gasar Borussia Dortmund ta lallasa Hanover ci 5-1 wanda kuma ya ba ta nasarar tsallakewa zagayen quarter Final. Tuni dai Bayern Munich ta doke Augsburg a ranar Talata ci 2-0.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.