Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Yau za a zabi Gwarzon kwallon kafa na Duniya.

Yanzu haka ana shirin fara zaben Gwarzon wasan kwallon kafa na Duniya, wanda akafiwa lakabi da Ballon d’Or tsakanin Lionel Messi da Cristiano Ronaldo da kuma Andres Iniesta. Rahotannin na nuna cewa, tuni ‘Yan wasan suka tashi zuwa birnin Zurich dake kasar Switzerland, inda ake sa ran za a ba da kyautar. 

Ronaldo (Hagu) Messi (Tsakiya) da iniesta (Dama)
Ronaldo (Hagu) Messi (Tsakiya) da iniesta (Dama) i2.cdn.turner.com
Talla

Masu horar da ‘Yan wasa da ‘Yan jarida da Kyaftin-Kyaftin ne zasu kada kuri’unsu a tsakanin ‘Yan wasan.

Dayawa na ganin cewa Messi wanda sau uku yana lashe kyautar zai sake karbeta a wannan karo ma.

Ita dai kyautar ta Ballon d’Or a shekarar 1965 Mujallar France Football ta fara da ita, a kuma shekarar 2010 aka hada kyautar da kyautar gwarzon kwallon kafa na duniya da hukumar FIFA ke bayarwa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.