Ingila
Aston Villa ta sha kashi a hannun Bradford
A gasar kalubalen Ingila karamar Kungiya Bradford City ta lallasa Aston Villa ci 3-1 a wasan kusa da karshe a karawar Farko. Bradford dai ta neman zama kungiya ta farko daga rukunin league din Ingila mataki na Hudu da ke neman buga wasan karshe tun bayan kungiyar Rochdale a 1962.
Wallafawa ranar:
Talla
A kwanakin baya ma dai Arsenal da Wigan ba su sha da di ba a hannun Bradford.
A yau Laraba ne Chelsea za ta karbi bakuncin Swansea City a Stamford Bridge.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu