Isa ga babban shafi

Bayern Munich ta kulla yarjejeniya da Guardiola

Kungiyar Bayern Munich ta Jamus ta dauki tsohon kocin Barcelona Pep Guardiola a matsayin kocinta wanda zai karbi aikin horar da ‘yan wasan kungiyar idan an kammala kakar wasa a watan Juni.

Tsohon Kocin Barcelona Pep Guardiola a lokacin da ya lashe kyautar gwarzon koci na Duniya
Tsohon Kocin Barcelona Pep Guardiola a lokacin da ya lashe kyautar gwarzon koci na Duniya REUTERS/Christian Hartmann
Talla

A lokacin da Guardiola yana Barcelona ya lashe kofuna da dama, kuma Bayern Munich ta dauke shi ne domin kawo karshen yunwar kofin da ta ke yi a shekaru biyu da suka gabata.
Tuni dai rahoranni daga Birtaniya suka ce Attajirin Chelsea Roman Abramovich ya yi wa Guardiola tayin makudan kudade don ya amince da aikin horar da Chelsea.

Amma wasu Rahotannin daga Jamus sun ce Guardiola ya kulla yarjejeniya ne da Bayern har zuwa 2016 domin nuna bajintar shi a kungiyar kamar yadda ya nuna Barcelona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.