Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Najeriya, Burkina Faso sun tsallaka zagayen kusa da karshe, Cote d’Ivoir da Togo sun kama hanyar gida

Nigeria da Burkina Faso sun tsallaka zuwa zagayen kusa da na karshe a cigaba da gasar cin kofin Nahiyar Afrika da ake gudanarwa a Afrika ta Kudu. Najeriya dai ta kara ne da Cote d’Ivoir, wadda ita ce kasa da wasu da dama ke tsammanin zata lashe kofin gasar inda ta sha kayi da ci 2-1.  

'Yan wasan Najeriya suna murnar lashe wasansu da Cote d'Ivoir inda suka ci 2-1
'Yan wasan Najeriya suna murnar lashe wasansu da Cote d'Ivoir inda suka ci 2-1 REUTERS/Mike Hutchings
Talla

Ita kuwa Burkino Faso ta lallasa kasar Togo ne bayan fafatawar da ta yi da Togo wadda ta kai ga karin lokacin bayan an tashi canjaras da lokaci ya cika, inda Jonathan Pitroipa ya zira kwallo a ragar Togo.

A yanzu haka Najeriya zata kara ne da Mali a ranar Laraba mai zuwa a birnin Durban sannan Burkino Faso zata kara da Ghana wadda sau hudu tana lashe kofin gasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.