Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Ingila ta doke Brazil 2-1, Jamus ta lallasa Faransa 2-1

A karon farko cikin shekaru 23 da suka gabata, Ingila ta samu nasarar farko akan ‘Yan wasan Brazil a jiya Laraba, bayan an buga wasan sada zumunci tsakanin kasashen biyu inda Ingilan ta lallasa Brazil da ci 2-1 a filin wasan Wimbledon. Wayne Rooney ya fara zira kwallon farko a ragar Brazil koda yake ta farke kwallon jim kadan bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, sai dai Frank Lampard ya kara zira kwallon da ta ba Ingila nasarar wasan daga baya. 

Rooney da Gerrard suna tafawa bayan Rooney ya zira kwallo a ragar Poland
Rooney da Gerrard suna tafawa bayan Rooney ya zira kwallo a ragar Poland REUTERS/Darren Staples
Talla

A farkon fara wasan dai Ronaldinho ya zubar da wata penalty da aka ba Brazil kamin Ingilan ta zira kwallon ta ta farko.

Sauran sakamakon wasannin sada zumunci a sassa daba daban na duniya na nuna cewa, Jamus ta doke Faransa da ci 2-1, a yayin da Ecuador ta doke Portugal da ci 3-2.

Wasa tsakanin Netherland da Italy an tashi ne da ci daya-da- daya, kana kasar Girka dad a Switzerland suka tashi babu ci kodaya, a yayin da Belgium ta doke Slovakia da ci 2-1.

Wasa tsakanin Croatia da Korea ta Kudu kuwa an tashi ne da 4-0, inda Croatia ta samu nasara, kana Ukraine kuwa ta doke Norway da ci 2-0, a yayin da Argentina ta doke Sweden da ci 3-2.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.