Isa ga babban shafi
Champions League

Arsenal za ta kara da Bayern Munich bayan ta fice gasar FA

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya mayar da martani ga koken da magoya bayan Arsenal ke yi akan shi bayan ya sha kashi a gasar FA Cup a hannun Blackburn. Sannan kocin ya yi watsi da rahoton jaridar The Sun game da tsawaita yarjejenitar shi ta shekaru Biyu.

Arsène Wenger Kocin kungiyar Arsenal ta Ingila
Arsène Wenger Kocin kungiyar Arsenal ta Ingila
Talla

An kwashe lokaci mai tsawo Arsenal na yunwar kofi, kuma a bana wata karamar kungiyar ce Bradford ta yi waje da Arsanal a Carling Cup kafin ‘Yan wasan Gunners su sake shan kashi a hannun Blackburn a gasar FA.

Arsene Wenger ya fuskanci suka da zagi daga magoya bayan Arsenal bayan sun sha kashi ci 1-0 a hanun Blackburn.

Bayan Arsene Wenger ya mayar da Martani, wasu rahotanni suka ruwaito za’a sabunta kwangilar shi ta shekaru Biyu, al’amarin da ya fusata kocin.

“Wannan rahoton karya ne, na cancanci yabo domin na yi aiki a Ingila tsawon shekaru 16” inji Wenger a lokacin da ya ke fuskantar suka da tambayoyi daga ‘Yan jaridu.

A yau Talata ne a gasar Zakarun Turai, Arsenal za ta kara da Bayern Munich da ke jagorancin Teburin Bundesliga kuma Arsene Wenger yace ya yi imanin ‘Yan wasan shi za su fitar da shi kunya duk da barakar da suke fuskanta a gida.

Manchester United ta tsallake zuwa zagayen Kwata Fainal bayan doke Reading ci 2-1. Kuma Sir Alex Ferguson ya godewa Nani wanda ya taimakwa Manchester United samun nasara a wasan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.