Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Bayern Munich ta doke Dortmund, Marseille ta sha kashi a hannun PSG

A gasar cin kofin kasar Jamus Bayern Munich ta doke Borussia Dortmund ci 1-0 a zagayen Kwata Fainal. PSG ta sake lallasa Marseille ci 2-0 a gasar neman lashe kofin Faransa. A gasar Copa Del Ray, Kungiyar Atletico Madrid ce za ta kara da Real Madrid a wasan karshe bayan doke Savilla da jimillar kwallaye ci 4-2.

Zlatan Ibrahimovic da David Beckham a tawagar PSG
Zlatan Ibrahimovic da David Beckham a tawagar PSG AFP
Talla

Bayern Munich ta huce hushin bara ne domin ta rama kashin da ta sha ne a hannun Borussia Dortmund ci 5-2 a wasan karshe.

A shekaru biyu da suka gabata, Borussia Dortmund ita ce ta mamaye jagorancin Teburin Bundesliga amma a bana tazarar maki 17 ne Bayern Munich ta ba Dortmund a teburin gasar.

Spain

A gasar Copa Del Ray, Atletico Madrid ta doke Savilla da jimillar kwallaye ci 4-2 bayan tashi wasa ci 2-2 a daren jiya.

Yanzu Atletico Madrid ce za ta kara da Real Madrid a wasan karshe, bayan Real Madrid din ta fitar da Barcelona a ranar Talata.

Faransa

Zlatan Ibrahimovic ya taimakawa PSG sake lallasa Marseille ci 2-0 a gasar neman lashe kofin kasar bayan doke Marseille din ci 2-0 a League.

Yanzu PSG za ta kara ne da Lorient wacce ta doke Brest ci 3-0 kamar yadda Bordeaux da Nancy dukkaninsu suka tsallake zuwa Kwata Fainal. Tun a jiya ne kuma Saint-Etienne ta doke Lille 3-2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.