Isa ga babban shafi
Champions League

Bayern Munich za ta karbi bakuncin Arsenal

Kungiyar Arsenal ta Ingila za ta kai wa Bayern Munich ziyara a kasar Jamus tare da fatar rama kashin da ta sha ci 1-3 a filin wasa na Emirates. Arsene Wenger na Arsenal yace abu ne mai yiyuwa su rama kashin da suka sha a gida.

kocin Bayern Munich tare da 'Yan wasan shi suna horo kafin su kara da Arsenal.
kocin Bayern Munich tare da 'Yan wasan shi suna horo kafin su kara da Arsenal. REUTERS/Eddie Keogh
Talla

“Abu ne mai wahala, amma mai yiyuwa ne kuma hanya daya da hakan zai yi yu shi ne taka wasa iya kwarewarmu, ina da kwarin giwar ‘yan wasa na za su kwantar da hankalinsu don samun nasara. Kuma ai wasa, wasa ne komi na iya faruwa” inji Arsene Wenger.

Bayern Munich dai ita ce ke jagorancin teburin Bundesliga da tazarar maki 20. Amma a yau Laraba Arsenal na iya samun sassauci domin akwai manyan ‘yan wasan kungiyar da aka haramtawa buga wasan da suka hada da Bastian Schweinsteiger da Jerome Boateng da kuma Franck Ribery wanda ke jinya.

Hakan ne dai yasa kocin Bayern Munich ya gargadi ‘yan wasan shi.

A daya bangaren kuma, Kungiyar Malaga ta Spain za ta yi kokarin rama kashin da ta sha ne a gidan FC Porto ci 1-0

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.