Isa ga babban shafi
Champions League

Bayern Munich da Malaga sun fitar da Arsenal da FC Porto

Arsenal ta rama kashin da tasha a hannun Bayern Munich amma ta fice gasar zakarun Turai bayan an tashi wasa ci 2-0 a Allianz Arena inda Bayern Munich ta tsallake saboda kwallaye uku da ta zira a ragar Arsenal a Emirates.

Dan wasan Arsenal Tomas Rosicky ya dafe kai bayan kammala wasa da Bayern Munich a Munich
Dan wasan Arsenal Tomas Rosicky ya dafe kai bayan kammala wasa da Bayern Munich a Munich REUTERS/Michaela Rehle
Talla

Yanzu haka dai an kori kungiyoyin Ingila gaba daya a gasar zakarun Turai bayan ficewar Arsenal, wanda wannan ne karon farko tun kakar wasa ta 1995-96 da za’a fafata a zagayen kwata Fainal ba tare kungiyoyin na Ingila ba.

Kungiyar Chelsea da Manchester city tun a zagayen farko ne suka fice daga gasar. A yayin da kuma Arsenal ta bi sahun Manhcester United a hanyar ficewa a zagaye na biyu, bayan sun sha kashi a hannun Bayern Munich da Real Madrid.

Amma Duk da Arsenal ta fice gasar Zakarun Turai, kocin kungiyar Arsenae Wenger yace ‘yan wasan shi sun fitar da shi kunya domin sun doke Bayern Munich a gidanta.

Arsene Wenger yace yana fushi da duk wani magoyi bayan Arsenal da ke fushi da rashin samun nasarar zira kwallo ta uku domin samun hurumin tsallakewa a zagayen Kwata Fainal.

A daya bangaren kuma kungiyar Malaga ta yi waje da FC Forto da jimillar kwallaye ci 2-1.

A daren jiya Malaga ta doke Porto ne ci 2-0 bayan Malaga ta sha kashi ci 1-0 a Portugal.

Hakan ke nuna kungiyoyin Spain uku ke nan suka tsallake zuwa zagayen kwata Fainal, Real Madrid da Barcelona da kuma Malaga.

Sai dai kocin Kungiyar Malaga yace yana fatar kada a hada shi wasa da Real Madrid ko Barcelona a zagayen Kwata Fainal.

A gobe Juma’a ne dai za’a hada kungiyoyin da zasu kara da juna a gasar Zakarun Turai zagayen Kwata Fainal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.