Isa ga babban shafi
Champions League

Bayern Munich za ta sake kece raini da Juventus, Gala da Madrid

Kungiyar Galatasaray ta Turkiya tana iya rubuta sabon Tarihi idan har ta rama kwallaye uku da Real Madrid ta jefa a ragarta a karawa ta farko amma kuma a Tarihin gasar Zakarun Turai, ba’a taba samun galabar Mourinho ba a zagayen kwata Fainal wanda ke neman lashe kofin karo na uku a kungiyoyi uku a kasashe daban daban.

José Mourinho, Kocin Real Madrid a Spain
José Mourinho, Kocin Real Madrid a Spain Reuters
Talla

Amma kocin Galatasaray Fatih Terim yace suna iyawa.

Galatasaray za ta buga wasan ne ba tare da wasu zaratan ‘Yan wasanta ba, Burak Yilmaz, wanda ya jefa kwallaye 8 a gasar Turai a bana, da kuma dan kasar Kamaru Dany Nounkeu mai tsaron baya.

A karshen mako Real Madrid ta lallasa Lavente ci 5-1, wanda hakan sako ne ga Galatasaray.

Akwai kuma wasa tsakanin Malaga ta Spain da Borussia Dortmund.

Wannan wasan dai na zuwa ne bayan mutuwar mahaifin kocin Malaga Manuel Pellegrini Wanda aka aiko masa da sakon mutuwar bayan sun sha kashi ci 4-2 a hannun Real Sociedad a karshen mako.

Wannan ne dai karo na farko da Malaga ta samu nasarar tsallakewa zuwa zagayen kwata Fainal a gasar zakarun Turai, amma a karawa ta farko Malaga da Dortmund sun tashi ne babu ci 0-0.

A gobe ne kuma Barcelona za ta karbi bakuncin Paris Saint-Germain, a yayin da kuma Juventus zata fafata da Bayern Munich.

A bana dai kungiyoyin Spain uku ne ke a ke fafatawa da su da kuma kungiyoyin Jamus guda biyu. Wannan ne kuma karo na farko da ake buga zagayen kwata Fainal ba tare da kungiyoyin Ingila ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.