Isa ga babban shafi
Premier League

West Ham ta rike United, Chelsea ta lallasa Fulham

West Ham ta rike Manchester United a Upton Park ci 2-2 wanda hakan ya rage wa Red Devils kwanakin yin bukin lashe kofin Premier karo na 20. Amma Kocin West Ham Sam Allardyce ya zargi alkalin wasa da haramta masu samun nasara akan United don tsira da maki uku.

'Yan wasan Manchester United Robin van Persie da Wayne Rooney.
'Yan wasan Manchester United Robin van Persie da Wayne Rooney. REUTERS/Eddie Keogh
Talla

Kungiyar Chelsea kuma ta lallasa Fulham ne ci 3-0. Jagoran kungiyar John Terry shi ne ya zirara kwallaye biyu bayan David Luiz ya jefa kwallo ta farko

Carlos Tevez kuma ya taimakawa Manchester City doke Wigan ci 1-0, hakan ne ya datse yawan makin da ke tsakanin City da United zuwa maki 13 a teburin Premier

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.