Isa ga babban shafi
Wasanni

Borussia Dortmund ta haramtawa Real Madrid zuwa wasan karshe na gasar Zakarun Turai

Kungiyar Borussia Dortmund ta tsallaka zuwa wasan karshe na cin kofin zakarun nahiyar Turai, wato Champions League, bayan da suka tashi Real Madrid na da ci 2 Borussia na nema, a karawa ta 2, ta wasan kusa da na karshe, tsakanin ta da Real din. Borussia ta sami wanan nasarar ne, bayan jimilar yawan kwallayen data samu sun zama 4, a kan 3 da Real ke da su.Real Sun yi ta kai kora a gidan Borussia, amma ba nasara, sai a daidai mintoci 82 da fara wasa, sannan Karim Benzema ya sami zura kwallon farko, ‘yan mintoci kadan kuma bayan nan, Sergio Ramos ya jefa ta 2.Wannan shine karo na 2 da Borussia Dortmund za ta je wasannin karshe na Champions League cikin shekaru 16.A shekarar 1997, suka fara zuwa wasan karshen, sai kuma wannan karon da suka sami nasara.

'Yan wasan Borussia Dortmund suna murnar samun nasara kan Real
'Yan wasan Borussia Dortmund suna murnar samun nasara kan Real REUTERS/Ina Fassbender
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.