Isa ga babban shafi
EUFA

EUFA ta dauki matakin Haramtawa dan wasa buga wasanni 10 saboda nuna Wariya

Hukumar kwallon EUFA a Turai ta cim ma matsayar yanke hukuncin haramcin wasanni 10 ga duk dan wasan da aka kama da laifin nunawa wani dan wasa wariyar launin fata saboda matsalar ta yi kamari a Turai.

Shugaban EUFA, Michel Platini tare da sakataren hukumar
Shugaban EUFA, Michel Platini tare da sakataren hukumar REUTERS/Valentin Flauraud
Talla

A Nahiyar Turai Bakaken fata suna fuskantar wariya inda ake kiransu da sunan Birai.

Hukumar EUFA tace zata dauki matakin rufe filin wasa na wuccin gadi idan har aka samu magoya bayan kungiyar da laifin nunawa ‘yan wasa wariya launin fata.

Kwamitin zartarwar hukumar ne ya amince da wannan matakin a wani taron da mambobin kwamitin suka gudanar a Birnin London.

A wata sanarwa kuma daga Hukumar ta EUFA an bayyana cewa a filin wasan Olympic a birnin Barlin na kasar Jamus za’a gudanar da wasan karshe na gasar zakarun Turai.

A karshen makon nan ne ranar Assabar za’a yi gamuwar kace raini domin lashe kofin gasar Zakarun Turai a filin wasa na Wembley tsakanin manyan kungiyoyin Jamus guda biyu Bayern Munich da Borussia Dortmund.

Karawar kungiyoyin biyu dai wata sabuwar adawa ce aka sabunta ko ake kokarin farfadowa tsakanin Borussia Dortmund da Bayern Munich wadanda suka mamaye gasar Bundesliga tsawon shekaru 40.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.