Isa ga babban shafi
Premier League

Gerrard ya sake kulla yarjejeniya da Liverpool

Steven Gerrard ya sake kulla sabuwar yarejejeniyar shekaru biyu da kungiyar Liverpool da ya fara rayuwa kafin yarjejeniyar shi ta kawo karshe a badi, kamar yadda shafin kungiyar ya ruwaito.

Jagoran Liverpool Steven Gerrard
Jagoran Liverpool Steven Gerrard
Talla

Steven Gerrard shi ne jagaran ‘Yan wasan Liverpool kuma dan wasan yace tsawaita yarjejeniyar abin farin ciki ne wanda ya fara wasa a Anfield a shekarar 1998.

A shekarun baya dan wasan ya nemi ya fice Liverpool bayan ya lashe kofin zakarun Turai, inda ya nemi ya koma Chelsea kafin ya daidaita da Liverpool.

Wannan sabuwar yarjejeniyar ta Steven Gerrard na zuwa ne a dai dai lokacin da kungiyar Arsenal ke ikirarin sabunta farautar da ta ke wa abokin wasan shi Luis Suarez.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.