Liverpool ta amince Luis Suarez ya tattauna da Arsenal
Kungiyar Liverpool ta kasar Ingila ta ce ta amince dan wasanta Luis Suarez ya bude tattaunawa da kungiyar Arsenal wacce ta taya shi akan kudi miliyan 40 na kudin pam din Ingila.
Wallafawa ranar:
Wannan tayi na Arsenal ya bude wata dama ce da za ta bawa dan wasan ficewa daga kungiyar ta Liverpool amma hukumomin kungiyar sun ce kudin da Arsenal din ta yi tayin ya yi kadan.
Rahotanni na nuna cewa, Liverpool na neman kudi miliyan 50 ne na pam din Ingila.
A daya bangaren a jiya ne Suarez ya dawo bugawa Liverpool wasa bayan kammala hukuncin da ya haramta mai buga wasannin guda goma da aka zartar bayan an same shi da laifin cizon dan wasan Chelsea, Branislav Ivanovic a kakar wasan da ta gabata.
Liverpool ta buga wasan sada zumunci ne da Melbourne Victory inda ta lallasa ta da ci 2-0.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu