CAF
Burundi ta tsallake zuwa CHAN
Kasar Burundi ta tsallake zuwa gasar cin kofin Afrika na kasashe 16 da za’a gudanar a kasar Afrika ta kudu a watan Janairun badi, Bayan ta doke Sudan ci 4-3 a bugun daga kai sai mai tsaron gida. Sauran kasashen da suka tsallake sun hada da Burkina Faso da Congo da Habasha da Ghana, Libya da Mali da Mauritania da Morocco, Najeriya da Uganda da kuma Afrika ta kudu mai masaukin baki, akwai kuma Kamaru da zata haska bayan dage mata takunkumi.
Wallafawa ranar: