Wasanni
Yelena Isinbayeva ta lashe zinare a wasan tsallen Pole Vault
‘Yar wasan jefa kibiya na Pole Vault ‘yar kuma kasar Rasha, Yelena Isinbayeva ta lashe zinare a wasan tsallan Pole Vault yayin da ake gudanar da gasar wasannin da ake yi a Rasha.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Talla
Wannan shine dai nasara da ta fara samu a fagen gasar duniya tun bayan nasarar da ta samu a wasan Olympic na Beijing a shekarar 2008.
“Wannan itace nasara mafi dadi a gare ni” Inji ta.
Isinbayeva ta kuma bayyana cewa za ta dauki hutun watanni 18 domin ta haihu inda take sa ran za ta dawo karawa a wasan Olympics na 2016 a Rio.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu