Kwallon kafa
An buga wasan kwallon kafa na farko a Afghanistan
A karon farko cikin shekaru 10, an buga wasan kwallon kafa a kasar Afghanistan tsakanin ‘yan wasan kasar da kuma na Pakistan inda Afgahnistan ta lallasa Pakistan da ci 3-0.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Talla
Bangarorin biyu sun kara ne a wani filin wasa mai daukan ‘yan kallo 6000 inda rahotanni ke nuna cewa an samu turuwa a wajen sayen tikitin shiga kallon wasan.
Rabon dai da kasar ta Afghanistan ta buga wasa a cikin gida tun a shekarar 2003.
Kuma rabon da kasashen biyu, su kara tun a shekarar 1997.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu