Isa ga babban shafi
La liga

Barcelona ta fara neman Casillas na Madrid

Jaridun Spain sun kwarmato cewa wai mai tsaron gidan Real Madrid Iker Casillas, Barcelona ta fara nemansa duk da tsawon shekarun da ya kwashe yana adawa da kungiyar inda wasu suke ganin hakan ba zata faru ba.

Iker Casillas, Mai tsaron gidan Real Madrid
Iker Casillas, Mai tsaron gidan Real Madrid Reuters
Talla

Casillas ya yi haskawa sau 654 a tawagar Madrid, inda ya lashe kofunan La liga guda biyar da kofin zakarun Turai biyu da kuma kofin Copa del ray.

Kuma Casillas yana cikin tawagar Galaticos a baya da suka kunshi Zidane da Ronaldo na Brazil da Figo, Amma Jaridun Spian a yankin Catalonia sun ruwaito cewa shugaban Barcelona Sandro Rosell yana tunanin daukar Casillas domin maye gurbin Valdes wanda zai fice a karshen kaka.

Tun a kakar wasan da ta gabata ne makomar dan wasan ke tangal tangal saboda yadda Mourinho ya fara ajiye shi a benci yana amfani da Diago Lopez a madadin shi, lamarin da ya haifar da sabani a tsakaninsu.

Haka kuma a farko fara La liga a bana, sabon kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya ajiye Casillas a saman benci a wasan da suka doke Betis ci 2-1 a Bernabeu. Kodayake kocin yace ya yi haka ne ba da wata manufa ba.

Wasu dai suna ganin yana da wahala dan wasan ya koma Barcelona saboda adawa amma idan muka koma Tarihi, Luis Figo ya koma Madrid daga Barcelona, haka ma Luis Enrique ya baro Real Madrid zuwa Barcelona a 1996.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.