Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Madrid ta doke Getafe, Balotelli ya barar da Fanalty

Cristiano Ronaldo ya taimakawa Real Madrid doke Getafe ci 4-1 a La liga a Spain inda ya zira kwallaye biyu a raga yayin da kuma Isco da Pepe suka zira sauran kwallayen. A Karon farko kuma Mario Balotelli ya barar da bugun daga kai sai mai tsaron gida a rayuwar shi.

Dan wasan AC Milan Mario Balotelli a lokacin da Pepe Reina mai tsaron gidan Napoli ya kabe kwallon shi a bugun daga kai sai mai tsaron gida
Dan wasan AC Milan Mario Balotelli a lokacin da Pepe Reina mai tsaron gidan Napoli ya kabe kwallon shi a bugun daga kai sai mai tsaron gida REUTERS/Alessandro Garofalo
Talla

Barcelona ce ke jagorancin teburin La liga da maki 15 kuma ta dare teburin ne da yawan kwallaye tsakaninta da Atletico Madrid da ke a matsayi na biyu ita ma da maki 15. Kungiyoyin biyu sun ba Madrid maki 2.

A ranar Assabar ne Barcelona ta lallasa Rayo Vallecano ci 4-0 amma kuma a wasan an fi Barcelona yawan taba kwallo, Wanda tarihi ne Vallecano ta karya na Barcelona tsawon shekaru biyar.

Faransa

Kungiyoyi masu hammayar Teburin gasar League 1, PSG da Monaco sun yi kunnen doki ne tsakaninsu, Inda Ibrahimovic ya fara zirawa PSG kwallo a raga amma daga bisani Falcao ya barke kwallon.

Yanzu dai Manoco ce ke saman teburin Legue 1 da maki 13.

Italiya

A Seria A, Mario Balotelli ya barar da Fanalty a karon farko a rayuwar shi inda AC Milan ta sha kashi ci 2-1 a hannun Napoli.

Jamus

A Bundesliga Bayern Munich ta lallasa Schalke ci 4-0 wanda ya ba ta damar haurowa dab da dare teburin gasar kusa da Borussia Dortmund da suke da maki 16 tsakaninsu.

A karshen makon nan Dortmund ta yi kunnen doki ne tsakaninta da Nuremberg wanda hakan ya datse yawan makin da ke tsakaninta da Bayern Munich.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.