Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Najeriya, Cote d’Ivoir da Kamaru sun sami shiga gasar cin kofin duniya

A karshen makon da ya gabata ne kasashen Najeriya da Cote d’Ivoir da kuma kamaru suka samu gurbin shiga gasar cin kofin duniya.

'Yan wasan Najeriya na murnar doke Ethiopia a birnin Calabar, an tashi a wasan da ci 2-0
'Yan wasan Najeriya na murnar doke Ethiopia a birnin Calabar, an tashi a wasan da ci 2-0 Reuters
Talla

Najeriya dai ta lallasa Ethiopia ne da ci 2-0, Cote d’Ivoir kuwa ta tashi ne da ci 1-1 tsakaninta da Senegal yayin da Kamaru mamayi Tunisia da ci 4-1 a wasannin da aka buga a zagaye na biyu na shiga gasar.

A nahiyar yanzu ya rage gurabe biyu inda ake sa ran kasashe biyu za su sake samun nasara a tsakanin karawar da za a yi da Ghana da Masar a gobe Talata da kuma karawa tsakanin Burkina Faso da Alegria.

Ita dai Ghana ta lallasa Masar da ci 6-1 a wasan farko yayin da Burkina Faso ta lallasa Algeria da ci 3-2 a wasan farko.

To yanzu haka a nahiyar Turai kasashen Italiya da Netherlan da Jamus da kuma Belgium suma sun samu damar shiga gasar.

Har ila yau Spain Ingila da Rasha da kuma Bosnia suma sun samu nasarar zuwa Brazil.
Yanzu ana jiran sakamakon karawa tsakanin Faransa da Ukraine, Girka da Romania, Portugal da Sweden da kuma karawa tsakanin Iceland da Croatia.

A nahiyar Asiya kuwa tuni Japan da Australia da Iran da kuma Korea ta Kudu suka suma suka sami wannan daman inda yanzu haka ake jiran Jordan da Uruguay.

A dai ranar shida ga watan Disamba mai zuwa ne ake sa ran za a karkasa kasashen da suka samu zuwa gasar zuwa rukuni rukuni domin kowa ya san da wanda zai fara karawa a gasar idan Allah ya kaima mu shekara mai zuwa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.