An hada City da Barcelona, Arsenal da Bayern Munich
Kungiyar Barcelona za ta kara da Manchester City a zagaye na biyu a gasar zakarun Turai, yayin da mai rike da kofin gasar Bayern Munich aka sake hada ta wasa da Arsenal karo na biyu a jere. Ana ganin wadannan ne wasanni mafi zafi da za'a gudanar a zagaye na biyu.
Wallafawa ranar:
Kungiyoyin Ingila Manchester United da Chelsea, sun samu sassauci daga kungiyoyin da aka hada su wasa a zagaye na biyu inda aka hada Manchester United wasa da Olympiakos ta Girka Chelsea kuma da Galatasaray ta Turkiya.
Kungiyar Paris Saint-Germain ta Faransa an hada ta wasa ne da Bayer Leverkusen ta Jamus, AC Milan kuma za ta kara ne Atletico Madrid.
An hada Real Madrid ne da Schalke 04 yayin da Borussia Dortmund zata kara da Zenit St Petersburg.
Didiar Drogba zai kai ziyara a Stamford Bridge inda Chelsea zata fara karbar bakuncin Galatasaray. Yaya Toure kuma zai kara ne da Tsohuwar kungiyar shi Barcelona.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu