Isa ga babban shafi
Wasanni

Man City ta sha kashi a hannun Barcelona yayin da PSG ta lallasa Leverkusen

A daren jiya talata Man City ta sha mummunan kashi a gaban dubban magoyan bayanta, a karawar da ta yi da Barcelona, wannan kuwa a ci gaba da fafatawa a gasar Neman Kofin Zakarun Nahiyar Turai.

Ibrahimovic na murnar zura kwallo a ragar Leverkusen a ranar 18 ga watan Fabarairun 2014
Ibrahimovic na murnar zura kwallo a ragar Leverkusen a ranar 18 ga watan Fabarairun 2014 REUTERS/Ralph Orlowski
Talla

An dai share tsawon mintuna 45 kafin a je hutun rabin lokaci, ba tare da wani ya zura kwallo a ragar wani ba.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne daya daga cikin ‘yan wasan Man City Martin Demichelis ya sa kafa ya sare Lionel Messi, wanda hakan ya sa aka ba shi jan kati tare da bai wa Barcelona bugun daga kai sai mai tsaron gida wato Penality, kuma Messi da kansa ne ya tashi daga faduwar da ya yi ya kuma shura kwallo sannan ta fada a raga ana miniti na 54.

Man City dai ta yi iya kokarinta domin rama wannan ci amma hakan ba ta samu narasa ba, yayin da ana gaf da tashi wasan, Dani Alves na Barcelona ya sake zura kwallo ta 2 a ragar City. Haka dai aka tashi wasan Barcelona na da kwallaye 2, Man City na nema.

Barcelona dai ta yi wannan tafiya zuwa Ingila ne da dukkanin shahrarrun yan wasanta, kamar Messi, Xavi, Iniesta, Fabragas Neymar da dai saurarunsu.

To sai dai manajan Man City Manuel Pellegrini, ya ce alkalin da ya hura wasan Jones Eriksson dan kasar Sweden, bai yi masu adalci ba, domin kuwa kamar ya rika fifita ‘yan wasan Barcelona tun daga farkon wasan har zuwa karshe, kuma wannan fifiko ne ya bai wa Barcelona nasara amma ba iya wasa ba.

Leverkusen da Paris Saint Germain

Wasa na biyu da aka buga a yammacin jiya shi ne tsakanin Bayer Leverkusen ta Jamus da kuma Paris Saint Germain ta Faransa, wasan aka buga a Jamus.

An dai tashi wasan ne PSG na da ci 4 Bayer na nema. Minti 3 da soma wasan ne Blaise Matuidi ya zura kwallo ta farko a ragar Bayer, inda aka ci gaba da fafatawa har zuwa minti na 39 lokacin da Zlatan Ibrahimovic ya zura kwallo ta 2.

Ibrahimovic ne dai ya sake zura kwallon ta 3 ta hanyar Penaliy sakamakon kuskuren dan wasan Bayer Emir Spahic ya yi har ma aka ba shi jan kati.

An dai ci gaba da wannan wasa tsakanin PSG da kuma Bayer Leverkusen har zuwa minti na 88 inda Faransawan suka kara zura kwallo ta 4 a ragar Jamusawa,. Sai a ranar 12 ga watan gobe na Maris ne dai za a je zagaye na biyu tsakanin wadannan kulob guda biyu, kuma za su hadu ne a filin wasa na Parc des Princes da ke Faransa.
 

Arsenal da Bayern Munich

A yammacin yau kuwa za a ci gaba da gasar ta Neman Kofin Zakarun Nahiyar Turai, inda Arsenal ta Ingila za ta karbi bakuncin Bayern Munich daga Jamus, yayin da ita kuma Atletico Madrid ta Spain za ta yi tatttaki zuwa Italiya domin karawa da AC Milan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.