Isa ga babban shafi
Wasanni

Man United ta sha kashi hannun Olympiakos, yayin da Borussia ta yi nasara kan St Peters

A ci gaba da gasar neman kofin Zakarun Nahiyar Turai a fagen kwallon kafa, a yammacin jiya an kara tsakanin Man United ta Ingila da kuma Olymiakos ta kasar ta Girka. Olympiakos ce ta yi nasara a wannan karawa inda aka tashi ci 2 da nema. 

Rooney na Mancherster U na kokarin zura kwallo a ragar Olympiakos
Rooney na Mancherster U na kokarin zura kwallo a ragar Olympiakos REUTERS/Alkis Konstantinidis
Talla

Sai wasa na biyu da aka buga daren na jiya tsakanin Borussia Dortmund ta Jamus da Zenith ST Petersburg ta Rasha. An dai buga wasan ne a gidan St Petersburg, to amma duk da haka wannan kulab ya sha kashi a hannun Burussia Dortmund ci 4-2.

A yammacin yau laraba kuwa, akwai wasanni biyu da ake shirin bugawa a gasar ta Zakarun Nahiyar Turai, inda za a yi karon batta tsakanin Real Madrid ta Spain da FC Schalke 04 ta Jamus, kuma za a buga wasan ne a gidan Schalke 04.

Daga cikin wadanda za su bugawa Madrid a wannan wasa har da Cirstiano Ronaldo, wanda sakamakon haramcin da aka sanya masa a can baya, aka buga wasanni 3 ba tare da ya samu damar fitowa a fillin kwallo ba sai a marecen yau.

Mai masaukin baki a wannan karawa wato Schalke 04, na a matsayi na 4 ne a teburin gasar Bundesliga a Jamus, yayin da Real Madrid ke matsayin na biyu a gasar La Liga.

Wata haduwar da ake shirin yi a marecen yau a gasar ta Zakarun Turai ita ce tsakanin Galatarasay ta Turkiyya da Chelsea ta Ingila, wasan da za a yi a kasar Turkiyya.

To sai dai abinda wata kila zai fi daukar hankulan masu shawarar wasan kwallon kafa shi ne, a yau tsohon shahrarren mai bugawa Chelsea Didier Drogba wanda a halin yanzu ke bugawa Galatasaray zai yi tozali da ‘yan wasan tsohon kulab din da ya yi suna a cikinsa wato Chelsea.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.