Costa zai fara taka kwallo a Spain
Diego Costa dan asalin kasar Brazil malamin raga a kungiyar Atletico Madrid zai fara bugawa Spain kwallo a karawar sada zumunci da Italiya bayan ya yi watsi da kasarsa Brazil.
Wallafawa ranar:
Spain zata kara ne da Italiya a ranar Laraba kungiyoyin da suka buga wasan karshe a gasar cin kofin Turai. Ana sa ran bayan kammala wasan kasashen zasu fitar da ‘Yan wasan da zasu kai ziyara a kasar Brazil a gasar cin kofin duniya.
A yau Talata, ya rage kwanaki 100 cur a fara gasar cin kofin Duniya a kasar Brazil. Kuma Samba boys ne na Brazil zasu fara karawa da Croatia a ranar 12 watan Yuni.
Costa ya taba sanya rigar Brazil a wasannin sada zumunci amma daga bisani dan wasan ya amince ya buga wa Spain kwallo.
A tsarin Hukumar FIFA, sai idan Dan wasa ya sanya riga a wata gasa shi ne ba zai iya canza sheka ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu