Isa ga babban shafi
Rasha-Paralympics

An soma wasannin nakkasassu a Sochi

A yau Juma’a ne za’a bude wasannin nakasssu na hunturu da ake kira Paralympics a kasar Rasha bayan kammala wasannin Olympics a makwanni biyu da suka gabata a Sochi .

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin a harabar wasannin Olympics na hunturu da aka gudanar a Sochi
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin a harabar wasannin Olympics na hunturu da aka gudanar a Sochi REUTERS/Mikhail Klimentyev/RIA Novosti/Kremlin
Talla

‘Yan wasa sama da 500 ne daga kasashe 45 zasu haska a wasannin domin lashe zinariya guda 72 a kwanaki 10 da za’a kwashe ana gudanar da wasannin.

Wannan ne dai karon farko da aka samu ‘yan wasa da dama fiye da wasannin da aka gudanar a shekarun baya, kusan tun fara wasannin a 1976.

Shugaban Rasha Vladimir Putin, ne zai bude wasannin a dai dai lokacin da ya ke fuskantar suka daga kasashen yammaci game da rikicin kasar Ukraine.

Amma wakilai da shugabannin kasashe musamman na yammaci da suka ce zasu kauracewa bikin bude wasannin saboda rikicin yankin Crimea da ake zargin Rasha ta yi kane-kane.

Birtaniya da Faransa sun ce zasu kauracewa bikin, kamar yadda Yarima Edward uban wasannin nakasassu na Birtaniya yace zai kaurace. Haka ma Laurent Fabius Ministan harakokin wajen Faransa yace babu Ministan kasar da zai kai ziyara a Rasha domin halartar bikin bude wasannin.

Cikin ‘Yan wasan da zasu gudanar da wasannin, akwai ‘Yan wasan Ukraine guda 31 da suka ce zasu ci gaba da wasanninsu, domin nuna wa duniya cewa Ukraine kasa ce mai cin gashin kanta.

A jawabinsa, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin yace yana fatar wasannin da za’a bude a yau a Sochi zasu sassauta barazana da tankiyar da ke tsakanin Rasha da Ukraine game da yankin Crimea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.