Isa ga babban shafi
Premier League

Vidic zai ci gaba da Jagorancin Manchester-Moyes

Kocin Manchester United David Moyes yace Nemanja Vidic ne zai ci gaba da jagorantar kungiyar har zuwa karshen kaka duk da Kungiyar Inter Milan a Seria A ta Italia ta tabbatar da cewa Dan wasan ya amince da yarjejeniya da ita idan an kammala kakar wasan bana.

Nemanja Vidic Jagoran Manchester United
Nemanja Vidic Jagoran Manchester United
Talla

Tuni dai Vidic yace zai yi bankwana da Old Trafford bayan ya kashe shekaru 8 yana taka kwallo a kungiyar Manchester United.

Moyes yace ficewar Vidic ba zai shafi mukamin shi ba a kungiyar.

Kungiyar Inter Milan tace Dan wasan ya sa hannu akan yarjejeniya da ita. Akwai kuma yiyuwar abokan wasan Vidic, Rio Ferdinand da Patrice Evra suna iya ficewa Manchester.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.