Isa ga babban shafi
Champions League

Barcelona da PSG sun yi waje da City da Leverkusen

Barcelona da PSG sun tsallake zuwa zagayen kwata Fainal a gasar zakarun Turai bayan sun samu nasara akan Manchester City da Bayer Leverkusen. Barcelona ta tsallake ne da jimillar kwallaye 4-1 a ragar Manchester City yayin da PSG ta lallasa Bayer Leverkusen da jmillar kawallaye 6-1 a kwarawar gida da waje.

Alkalin wasa Stephane Lannoy  ya ba Dan wasan Manchester City Pablo Zabaleta Jan kati a fafatawa da Barcelona a gasar zakarun Turai
Alkalin wasa Stephane Lannoy ya ba Dan wasan Manchester City Pablo Zabaleta Jan kati a fafatawa da Barcelona a gasar zakarun Turai REUTERS/Gustau Nacarino
Talla

A filin wasa na Nou Camp Alkalin wasa ya ba dan wasan City Pablo Zabaleta jan kati kuma yanzu Manchester City ita ce kungiya ta biyu daga Ingila da ta fice gasar bayan Bayern Munich ta yi waje da Arsenal.

Messi ne ya fara zirawa Barcelona kwallo a raga amma Vincent Kompany ya rama kwallon, daga bisani kuma ana dab da kammala wasan Dani Alves ya sake jefa kwallo ta biyu a ragar City.

PSG kuma tana neman zama kungiya ta biyu ce daga Faransa da zata lashe kofin gasar bayan kungiyar Marseille a shekarar 1993 bayan ta casa Bayer Leverkusen.

Kocin PSG Laurent Blanc ya gargadi ‘yan wasan shi su yi iya kokarinsu na samu nasara anan gaba yana mai cewa kada su yi tunanin zasu hadu da wata kungiya mai sassauci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.