Isa ga babban shafi
Premier League

Suarez ya lashe kyautar Kwararrun 'Yan wasa

Luis Suarez na Liverpool shi ne ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Ingila ta kungiyar kwararrun ‘Yan wasa, inda a bana dan wasan na Uraguay ya zirara kwallaye 30 a raga. Amma wannan kyautar na zuwa ne bayan Chelsea ta samu sa’ar Liverpool a Anfield ci 2 da 0 a karawar hamayya da suka yi na fafatikar lashe kofin Premier a bana.

Luis Suarez na Liverpool
Luis Suarez na Liverpool REUTERS/Nigel Roddis
Talla

Cikin jerin ‘Yan wasan da dai aka zaba guda 11 babu dan wasa daga kungiyar Arsenal da Manchester United amma ‘yan wasan Chelsea da Liverpool da Manchester City ne suka mamaye tawagar ta zaratan ‘Yan wasa 11 da kwararrun ‘Yan wasa suka zaba.

Kocin Manchester City Manuel Pellegrini yace ya yi imanin za su lashe kofin Premier a bana bayan ‘Yan wasan shi sun doke Crystal Palace xi 2-0.

Tazarar maki uku ne yanzu Liverpool da ke jagorancin teburin gasar ta ba Manchester City da ke matsayi na uku, amma City tana da kwantaen wasa guda. Maki guda ne kuma tsakaninta da Chelsea da ke matsayi na biyu a yanzu.

City dai na iya lashe kofin gasar da yawan kwallaye idan har ta samu nasara a sauran wasanninta da suka rage.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.