Real Madrid ta lallasa Bayern Munich
Real Madrid ta tsallake zuwa buga wasan karshe da jimillar kwallaye ci 5-0 a gasar zakarun Turai da za’a gudanar a birnin Lisbon a watan Mayu bayan ta bi Bayern Munich har gida da ke rike da kofin gasar ta lallasa ta ci 4-0 a karawa ta biyu da suka fafata a Allianz Arena a kasar Jamus.
Wallafawa ranar:
Real Madrid a bana tana fatar lashe kofin gasar ne karo na 10, a ranar 24 ga watan Mayu da za’a yi fafatawar karshe a Lisbon.
Tun kafin aje hutun rabin lokaci, Real Madrid ta yi ruwan kwallaye uku a ragar Bayern Munich.
Sergio Ramos ne ya fara jefa kwallaye biyu a raga, kafin daga bisani Cristiano Ronaldo ya ida cika kwallaye biyu a ragar Bayern Munich.
Cristiano yanzu ya zira kwallaye 16 a gasar zakarun Turai.
Wannan ne kuma ya ba Dan wasan na Duniya kafa wani sabon tarihi a matsayin dan wasa mai yawan kwallaye da ya zira a kaka guda a gasar zakarun Turai, inda ya sha gaban Messi na Barcelona da Altafini na AC Milan.
Kocin Bayern Munich Pep Guardiola ya dauki laifin dukan da Real ta yi wa ‘Yan wasan shi, wanda shi ne sakamakon wasa mafi muni ga Bayern Munich a gidanta.
Guardiola yace kuskurensa shi ne hada Bastian Schweinsteiger da Toni Kroos a tsakiyar Fili.
A yau Laraba ne kuma Chelsea da Atletico Madrid zasu kece raini da juna a Stamford Bridge domin tantance kungiyar da zata hadu da Real Madrid a wasan karshe.
A karawa ta farko, kungiyoyin biyu sun tashi wasa ne babu ci, a yayin da a yau dole a fitar da gwani a karawar kungiyoyin biyu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu