Jaridun Brazil sun yi sharhi a kori Scolari
Jaridun kasar Brazil sun yi sharhi game da tarbarewar kwallon kafa a Brazil tare da yin kira a gaggauta korar mai horar da ‘Yan wasan kasar Luiz Felipe Scolari wanda ya jagoranci ‘Yan wasan kasar a gasar cin kofin duniya da Jamus ta lallasa Brazil ci 7 da 1.
Wallafawa ranar:
Wasu Jaridun sun wallafa labari game da kocin na Brazil suna masa bankwana bayan Holland ta doke kasar ci 3 da 0 a wasan neman na uku.
Jaridun sun bayyana cewa wannan shi ne lokaci mafi muni a tarihin kwallon kafa a Brazil.
Scolari wanda ya jagoranci tawagar Brazil da suka lashe kofin duniya a 2002, yace yanzu ya rage ga hukumar kwallon Brazil ta yanke hukunci akan makomar shi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu