Isa ga babban shafi

Litinin za a kaddamar da Herve Renard a matsayin kocin Cote d'Ivore

An nada Herve Renard a matsayin sabon mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasar Ivory Coast, inda zai maye gurbin Sabri Lamouchi, daya ajiye aikin shi bayan kungiyar ta fice daga wasannin cin kofin duniya da aka a Brazil, tun daga zagayen farkon wasan. Ranar Litinin mai zuwa, za a kaddamar da Renard, mai shekaru 45 aduniya, inda zai sanya hannu kan wata kwataragin aiki ta shekaru 2, da ake fata zai yi amfani da ita wajen kai kasar zuwa wasan cin kofin nahiyar Africa.Sabon kocin, wanda dan kasar Faransa ne, ya dade yana aiki a Nahiyar Africa, sau dai yawanci yayi aikin ne a matsayin mataimakin mai koyar da ‘yan wasan, inda a baya bayan nan ya yi aiki a matsayin mataimakin mai koyar da ‘yan wasan kasar Ghana, Claude Leroy a shekarar 2007 zuwa 2008.Ya kuma kai Zambia gasar cin kofin nahiyar Aftrica a shekarar 2012, inda kuma yaran nashi suka yi nasara a Ivory Coast, a bugun daga kai sai mai tsaron gida a wasan karshe. 

sabon kociyan Ivory Coast, Herve Renard
sabon kociyan Ivory Coast, Herve Renard AFP PHOTO/ KHALED DESOUKI
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.