Zakarun Turai: Lille ta doke Grasshoppers
Standard Liege ta yi waje da Panathinaikos daga fafatawar neman hurumin shiga gasar zakarun Turai bayan ta doke kungiyar ta Girka ci 2 da 1. Duk da kuma Grasshoppers ta Swizerland ta rike Lille ta Faransa ci 1 da 1 amma bai hanawa Lille samun hurumin buga wasannin neman shiga gasar zakatun Turai ba, saboda nasarar da Lille ta samu ci 2-0 a karawa ta Farko.
Wallafawa ranar:
Bate Barisov ta Belarus da Maribor ta Slovenia dukkaninsu sun tsallake zuwa buga wasannin share fagen gasar zakarun Turai inda za’a buga sauran wasannin a yau Laraba kafin ranar Juma’a a hada kungiyoyin da zasu kara da juna.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu