Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Real Madrid ta lashe Super Cup

Real Madrid da ta lashe kofin zakarun Turai ta sake lashe kofin Super na Turai bayan ta doke Sevilla ci 2 da 0. Cristiano Ronaldo ne ya zirara dukkanin kwallaye biyu a ragar Sevilla da ta lashe kofin Europa League.

James Rodriguez na Real Madrid ya daga kofin Super a kusa da Ronaldo da Bale bayan sun doke Sevilla
James Rodriguez na Real Madrid ya daga kofin Super a kusa da Ronaldo da Bale bayan sun doke Sevilla REUTERS/Rebecca Naden
Talla

Ana fafata neman lashe kofin Super ne tsakanin Kungiyar da ta lashe kofin Zakarun Turai da kofin Europa League manyan gasanni guda biyu a Turai.

Ronaldo ya buga wasan ne tare da Benzema da Gareth Bale da kuma sabbin ‘Yan wasan da Real Madrid ta sayo a kasuwa a bana Toni Kroos da James Rodriguez wanda wannan zubin ‘Yan wasan a kungiya guda shi ne mafi tsada a tarihin kwallon kafa
Jimillar kudin ‘Yan wasan sun kai sama da euro Miliyan 310.

Wannan ne karo na biyu da Real Madrid ta lashe kofin na Super bayan lashe kofin a 2002.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.