Isa ga babban shafi
FIFA

Barcelona zata kalubalanci haramcin sayen ‘Yan wasa

Kungiyar Barcelona tace za ta kalubalanci haramcin sayen ‘Yan wasa da hukumar FIFA ta ki yin watsi da hukuncin bayan ta daukaka kara. Kungiyar tace hukuncin ya yi karo da mutuncin makarantar La Masia ta horar da matasa.

Tawagar  Kungiyar Barcelona da FIFA ta haramtawa sayen 'Yan wasa
Tawagar Kungiyar Barcelona da FIFA ta haramtawa sayen 'Yan wasa REUTERS/Albert Gea
Talla

Hukumar FIFA tace Barcelona ta keta dokokin sayen kananan yara. Kuma haramcin ya shafi kasuwar ‘Yan wasa biyu a jere, amma haramcin zai fara aiki daga watan Janairun badi.

Barcelona ta fadi a shafinta na Intanet cewa zata kalubalanci hukuncin a kotun sauraren koken wasanni CAS.

Barcelona za ta iya ci gaba da cin kasuwa kafin rufe kasuwar ‘yan wasa a yanzu, amma za’a shafe tsawon kasuwa biyu ba tare da ta saye sabbin ‘yan wasa ba.

A bara dai Barcelona an kammala kaka ba ta da kofi koda na shan ruwa, kuma wannan ana ganin yana da nasaba ga mataloli da suka daibaibaiye kungiyar a kakar da ta gabata da suka hada da rikicin siyasar shugabancin kungiyar da badakalar Naymar da kuma barazanar FIFA da ta kunno kai na dakatar da kungiyar shiga kasuwar ‘Yan wasa.

A kasuwar da ake ci yanzu, Barcelona ta dauko Luis Suarez da Ivan Rikitic da Thomas Vermaelen da Jaremy Mathieu da kuma masu tsaron gida guda biyu.

Amma Akwai barazana yanzu ga Barcelona na nemo wanda zai maye gurbin Xavi wanda ke shirin ficewa kungiyar a badi bayan Fabregas ya koma Chelsea.

Luis Suárez, Dan wasan da Barcelona ta saya daga Liverpool a bana.
Luis Suárez, Dan wasan da Barcelona ta saya daga Liverpool a bana. REUTERS/Gustau Nacarino

Alkawaullan da Barcelona ta kulla da ‘Yan wasa a wasu kungiyoyi a badi dole ta canza salo a yanzu, musamman batun Marcos Reus wanda ke fatar dawowa Barcelona idan kwangilar shi ta kawo karshe a Borussia Dortmund. Haka kuma Douglas Pereira na Soa Poulo da kungiyar ke son ya maye gurbin Dani Alves da zata sayar.

Dole dai Barcelona sai ta ware kudi yanzu domin tsunduma cikin kasuwar ‘Yan wasa kafin rufe kasuwar nan da kwanaki 10, in ba haka ba Real Madrid da Atletico Madrid da ke hammaya da Barcelona a Spain za su samu garabasa anan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.