Isa ga babban shafi

An baiwa Morocco zuwa Asabar ta dauki mataki kan wasan cin kofin Africa

Kasar Morocco nada nan zuwa ranar Asabar mai zuwa, ta yanke shawara, ko dai ta amince zata iya karbar bakuncin wasannin cin kofin nahiyar Africa na shekara mai zuwa ta 2015, ko kuwa a baiwa wata kasar damar daukar nauyin wasan. Dama Morocco ta nemi a dage wasan, da aka shirya yi daga ranar 17 ga watan Junairu zuwa 8 ga watan Fabrauru, saboda wai tana fargabar tururuwar da jama’a zasu yi zuwa kasar zai iya sanadiyyar samun barkewar Ebola, cutar da zuwa yanzu tayi sanadiyyar rasa ran mutane kusan 5000. 

Alamar gasar cin kofin nahiyar Africa da za ayi a Morocco cikin shekarar 2015
Alamar gasar cin kofin nahiyar Africa da za ayi a Morocco cikin shekarar 2015 CAN2015
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.