Isa ga babban shafi
Zakarun Turai

Madrid ta doke Liverpool, Anderlecht ta rike Arsenal

Real Madrid da Borussia Dortmund sun tsallake zuwa zagaye na biyu a gasar zakarun Turai bayan sun samu nasara a wasannin da suka fafata a jiya Talata duk da saura wasanni biyu a kammala karawar rukunin farko.

Karim Benzema, na Real Madrid da ya jefa kwallo a ragar Liverpool.
Karim Benzema, na Real Madrid da ya jefa kwallo a ragar Liverpool. REUTERS
Talla

Madrid ta sake doke Liverpool ci 1 da 0 a Bernabeu bayan ta doke ta ci 3 da 0 a Anfield.

Dortmund ta lallasa Galatasaray ne ci 4 da 1 a Jamus wanda ya ba ta damar jagorantar rukuninsu na D da maki 12.

Kungiyar Anderlecht ta Belgium kuma ta rike Arsenal ne ci 3-3 a Emirate. Arsneal bata sha da dadi ba domin ita ce ta fara jefa kwallaye uku, amma daga bisani Anderlecht ta farke kwallayen.

'Yan wasan Arsenal a karawarsu da  Anderlecht a gasar Zakarun Turai
'Yan wasan Arsenal a karawarsu da Anderlecht a gasar Zakarun Turai REUTERS/Eddie Keogh

Liverpool dai yanzu ta rikito kasa da jimillar maki uku a teburin rukuninsu, bayan Basel ta casa Ludogorets 4 da 0 a Switzerland.

A rukunin A kuma, Atletico Madrid ta Spain ta doke Malmo ne ta Sweden ci 2 da 0, yayin da kuma Juventus ta samu sa’ar Olympiakos ci 3 da 2.

A jiya ne Andrea Pirlo na Juventus ya yi haskawa ta dari a gasar zakarun Turai, wanda kuma ya fara jefa kwallo a raga.

Benfica kuma ta doke Monaco ne ci 1 da 0 a birnin Lisbon.

Bayer Leverkusen ta bi Saint Petersburg har gida Rasha ta doke ta ci 2 da 1.

A yau Laraba ma akwai ci gaba da fafatawa a gasar zakarun, inda Bayern Munich da PSG da Barcelona da FC Porto da Chelsea dukkaninsu za su yi fatar samun nasara domin tsallakewa zuwa zagaye na gaba.

Barcelona zata fafata ne da Ajax ta Holland inda Suarez zai kai ziyara tsohuwar kungiyar shi inda ya jefa kwallaye 111 kafin ya koma Liverpool.

PSG zata kara ne da Nicosia ta Cyprus, kuma PSG da Barcelona da ke jagorantar rukuninsu na F suna na iya tsallakewa zuwa zagaye na gaba idan sun samu nasara a yau.

Manchester City kuma zata karbi bakuncin CSKA Moscow ta rasha ne a Etihad a London.

Bayern Munich kuma zata tafi birnin Rome ne domin haduwa da Roma, wacce ta sha kashi ci 7-1 a Jamus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.