Isa ga babban shafi
FIFA

Jamus ce gwanin kwallon Kafa

Kasar Jamus ce ta farko a fagen kwallon kafa a duniya, a cikin jerin ajin matsayi da hukumar kwallon FIFA ta fitar a farkon sabuwar shekarar 2015. Jamus dai ta dare matsayi na farko ne tun lokacin da ta lashe kofin duniya a Brazil a bara.

Tawagar Jamus da suka lashe kofin duniya a Brazil
Tawagar Jamus da suka lashe kofin duniya a Brazil REUTERS/Michael Dalder
Talla

Argentina da ta fafata da Jamus a wasan karshe a Brazil ita ce a matsayi na biyu. Sai Colombia a matsayi na uku.

Belgium tana matsayi na hudu saman Netherlands da ke mastayi na biyar.

Brazil ce a matsayi na shida, yayin da Faransa da Portugal ke matsayi na bakwai, Spain ce a matsayi na 9, Uraguay a mastayi na 10.

Kasar Algeria ce ta farko a Afrika amma ta 18 a duniya. Najeriya tana matsayi ta 43 a duniya amma ta 8 a Afrika.

Nijar tana matsayi na 119.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.