Isa ga babban shafi
Wasanni

Gasar kofin kwallon kafar Afirka a Equatorial Guinea

A ranar asabar 17 ga watan janairu ne za a buda gasar neman kofin kwallon kafana nahiyar Afirka a karo na 30 a kasar Equatorial Guinea, gasar da za a ci gaba da yi har zuwa ranar 8 ga watan gobe na Fabarairu a tsakanin kasashe 16.

Tambarin hukumar kwallon kafar Afirka don gasar 2015
Tambarin hukumar kwallon kafar Afirka don gasar 2015
Talla

Kasar Guinea dai ta samu damar daukar nauyin gasar ne a cikin watan nuwambar da ya gabata bayan da Maroko ta bukaci a dage gasar saboda dalilai na fargabar yaduwar cutar Ebola.

To sai dai lura da cewa ba shi ne karo na farko da wannan karamar kasa mai yawan mutane dubu 740 ke daukar nauyin wannan gasa ba, hakan ya sa ake ganin cewa duk da kurewar lokaci ba za a samu wata matsala ba, domin kuwa a shekarar 2012, kasar da kuma Gabon sun dauki nauyin gasar.

Za a dai buga wasannin ne a filaye 4, wato birnin Bata, Malabo, Mongomo da kuma Ebebiyin, kuma tuni shugaban kasar Teodoro Obiang Nguema ya saye tikiti dubu 40 don bai wa jama’a shiga kallon gasar.

To sai dai wata babbar matsala da aka soma fuskanta a halin yanzu ita ce rashin masauki, domin kuwa tuni hotel suka cika makil da ‘yan wasa da kuma tawagoginsu.

Misali, kocin kulob din kasar Congo Brazaville daya daga cikin kasashen da ke halartar garar Claude Le Roy, ya ce kawo yanzu 5 daga cikin ‘yan tawagarsa su 35 har yanzu ba su samu masauki ba, sannan kuma akwai matsalar ruwa har ma da ta wutar lantarki a inda aka sauke sauran mutanensa.

Kasashe 16 ne dai ke halartar gasar da za a buda a ranar asabar, kuma tuni aka san wadanda za su kara da juna tun a zagayen farko.

Jim kadan bayan kammala bukin buda gasar a gobe, za a fara karawa ne tsakanin ;

-Equatorial Guinea-Congo Brazaville
-Sai Burkina Faso da za ta kara da Gabon

Ranar18 Janairu

-Zambia –Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo
-Tunisia da za ta fafata da Cape Verde

Ranar 19 Janairu

-Ghana za ta hadu da Senegal, sai kuma Algeria da za ta kece reni da Afirka ta kudu

Yayin da a ranar 20 Janairu

Cote D’ivoire za ta hadu da kasar Guinea Conakry, sai kuma Mali da za fafata da Kamaru
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.