Isa ga babban shafi
CAF

Issa Hayatou na son ya zarce

Rahotanni sun ce shugaban hukumar CAF Issa Hayatou yana neman a yi wa tsarin dokokin hukumar kwallon Afrika kwaskwarima domin ya samu damar yin tazarce kan madafan ikon hukumar.

Shugaban kwallon Afrika Issa Hayatou.
Shugaban kwallon Afrika Issa Hayatou. AFP PHOTO / STEPHANE DE SAKUTIN
Talla

A tsarin dokar hukumar CAF duk jami’in da ya kai shekaru 70 ya zama wajibi ya yi murabus, amma rahotanni sun ce Issa Hayatou yana neman a sabunta dokar a babban taron hukumar da za a gudanar a birnin Al Kahira a watan Afrilu duk da ya kwashe shekaru da dama yana shugabancin kwallon Kafa a Nahiyar Afrika.

Wa’adin shugabancin Hayatou zai kawo karshe ne a 2017 amma yana neman karin wa’adi har zuwa 2021, lokacin da shekarunsa suka zarce 75.

Tun shekarar 1988 ne Hyatou ke shugabancin CAF.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.