Copa del Ray
Barcelona ta kai zagayen karshe a Copa del Ray
Barcelona za ta hadu da Athletic Bilbao a wasan karshe a gassar Copa del Ray bayan kungiyoyin biyu sun samu nasara a wasanninsu da suka fafata a zagayen dab da na karshe. Barcelona ta lallasa Villarreal ne da jimillar 6-2.
Wallafawa ranar:
Talla
Kwallaye biyu Neymar ya zira a raga, yayin da Suarez ya jefa Barcelona kwallo ta uku a ragar Villarreal inda suka tashi ci 3 da 1 a jiya Laraba.
Yanzu jimillar kwallaye 11 Suarez ya jefa wa Barcelona.
Athletic Bilbao ta kai zagayen karshe ne bayan ta doke Espanyol da jimillar kwallaye ci 3-1.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu