Isa ga babban shafi
CAF U20

Flying Eagles sun nufi Senegal

‘Yan wasan Flying Eagles na Najeriya sun nufi Senegal domin fafatawa a gasar cin kofin matasa ta ‘yan kasa da shekaru 20. A karshen makon nan ne ‘Yan wasan na flying Eagles za su fara fafata wa da Senegal mai masaukin baki.

Tambarin Hukumar kwallon Najeriya NFF
Tambarin Hukumar kwallon Najeriya NFF completesportsnigeria.com
Talla

Hukumar kwallon Najeriya NFF ta bukaci ‘Yan wasan na Manu Garba su lashe kofin gasar a Senegal.

A gasar ‘Yan kasa da shekaru 17, da aka gudanar a Nijar, ‘yan wasan Eaglet ba su sha da dadi ba a matsayi na hudu yayin da matasan Mali suka lashe kofin gasar bayan sun doke ‘Yan wasan Afrika ta kudu.

Kasashe hudu da suka kai zagayen dab da na karshe su ne za su wakilci Afrika a gasar cin kofin duniya ta ‘yan kasa da shekaru 20 da za’a gudanar a a New Zealand da gasar ‘Yan kasa da shekaru 17 a Chile.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.