Isa ga babban shafi
wasanni

Benitez zai ci gaba da horar da Napoli

Shugaban Kungiyar Napoli ta Kasar Italiya, Aurelio De Laurentis ya bayyana cewa Kocin kungiyar, Refa Benitez zai cigaba da kasancewa a kan mukaminisa har na tsawon shekaru biyar masu zuwa duk da cewa kwantiraginsa zai kare ne a karshen wannan kakan wasannin

Kocin Napoli, Rafa Benitez
Kocin Napoli, Rafa Benitez Reuters
Talla

A hirar da aka yi da shi a wani gidan rediyo na kasar Italiya, Shugaban Kungiyar ya ce, idan Benitez ya amince da cigaba da jan ragamar kungiyar ta Napoli, to zai fi kowa farin ciki a fadin duniya.

Dama dai anata asashen nan da karshen kakan wasannin nan ne, Benitez zai bar Napoli, inda ake tunanin zai koma horar da manyan kungiyoyin kwallon kafa a Turai kamar su PSG da Manchester City.

A shekara ta 2013 ne, Banitez ya kulla kwantirgi da Napoli amma har yanzu dankinsa na zaune arewa maso yammacin Kasar Ingila.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.