Kwallon Kafa
Chelsea na dab da lashe Firimiya
Chelsea na dab da lashe kofin Firimiya bayan ta doke Leicester City 3 da 1 a jiya Laraba. Didier Drogba da John Terry da Ramires ne suka zirara wa Chelsea kwallayenta a raga, bayan Marc Albrighton ya fara jefa kwallo a ragarsu. A ranar Lahadi Chelsea na iya bikin lashe kofin gasar idan har ta doke Crystal Palace.
Wallafawa ranar:
Talla
Chelsea ta ba Manchester City da Arsenal tazarar maki 13 a teburin Firimiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu