Isa ga babban shafi
La liga

Za a ci gaba da wasannin La liga

Kotun Spain ta haramta wa manyan ‘Yan wasan kasar shiga yajin aiki domin kalubalantar sabon tsarin ‘yancin kudaden da ake samu daga kafofin Telebijin da ke nuna wasannin. Yanzu matakin na nufin Barcelona na iya lashe kofin La liga a karshen mako.

Tambarin gasar La liga a Spain
Tambarin gasar La liga a Spain
Talla

Kotun tace barazanar yajin aikin mataki ne da zai kawo tarnaki ga sauran wasannin La iga da suka rage a kammala gasar nan da ‘yan kwanaki.

‘Yan wasan dai sun yi barazanar shiga yajin aiki kan batun ba kananan kungiyoyi kudadan da ake samu daga nuna wasannin a Telebijin.

Kuma ‘yan wasa daga manyan kungiyoyi irinsu Iker Casillas na Real Madrid da Xavi da Andres Iniesta na Barcelona suna cikin wadanda ke jagorantar a shiga yajin aikin.

Amma hukumar kula da manyan lig din kasar guda biyu na ganin yajin aikin zai janyo mata hasarar kudade da suka kai euro miliyan 50 ga duk wasan da ba a buga ba a La liga.

Kotun tace zata ci gaba da nazari akan batun, kafin ta zartar da hukunci a watan Yuni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.