Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

AC Milan za ta kori Inzaghi

Shugaban Kungiyar AC Milan Silvio Berlusconi ya tabbatar da matakinsa na sallamar kocin kungiyar kuma toshon dan wasansa Filippo Inzaghi idan har an kammala kakar wasan bana, kamar yadda jaridun Italiya suka tabbatar.

Kocin AC Milan Filippo Inzaghi yana tattaunawa da alkalin wasa Piero Giacomelli
Kocin AC Milan Filippo Inzaghi yana tattaunawa da alkalin wasa Piero Giacomelli REUTERS/Alessandro Garofalo
Talla

Wannan matakin yana da nasaba da rashin katabus na kungiyar a bana karkashin jagorancin Inzaghi, wanda ya gaji abokinsa Seedorf a watan Yunin 2014.

Berlusconi yace suna jiran lokaci ne akwai su raba gari da Inzaghi.

Ana ganin dai wannan ce kaka mafi muni ga AC Milan bayan ta kasance matsayi na 11 a teburin Seria A a bana.

Jaridun Italiya sun kwarmato cewa Barlusconi yana nazari akan dauko Carlo Ancelotti wanda ake hasashen zai fice Real Madrid idan an kammala kaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.